Mugun Tanadin Masu Mamayar Duniya yahudu – Mal Bashir Ahmad Sani Sokoto


Wannan jawabin ya fito ne daga bakin Malamin addinin Musulunci masanin kimiyya Ash-sheikh Dr Bashir Ahmad Sani Sokoto cikin darasin tafsirin Qur’ani na ranar 6 ramadan 1441/2020.
Malam yace:
Na tabbatar da cewa wannan cutar ta Coronavirus su suka kirkireta, kuma su ke rike da maganinta, nan gaba zasu fitar da maganin, kuma zaku sayi maganin da makudan miyagun kudade, wannan yana daga cikin abinda suke kira da “Biological Warfare”, sune “Biological Weapons” makaman yaki da ake amfani dashi ta hanyar kirkira da yada miyagun cututtuka wanda duniya ta shaida akwai kasashe wadanda suke da wadannan makaman
Kasashen sun hada da Amurka (USA), sannan akwai Burtaniya (UK) suma suna da wannan makamin, akwai Kasar Faransa, akwai Kasar Jamus, akwai Kasar Japan itama tana da shi, akwai China, akwai kasashen da aka kirkiro aka laka musu sharri cewa suna da Biological Weapons domin a yake su, Iraqi ance tana dashi, an yaketa kuma anje ba’a gani ba, Libya ance Gaddafi yana da makamin, an kashe shi anje an duba ba’a gani ba
To haka nan akwai wasu sauran kasashe da yanzu ana fakonsu ana cewa suna da wannan makami na Biological Weapons, amma kuma gaskiyar lamari ba su da shi, anyi haka ne kawai domin wata manufa, domin nan gaba ana da manufar kai musu farmaki
Don haka akwai abinda ake kira da Biological Weapons, wanda za’ayi amfani da wasu Organisms ko wani abu wanda yake iya manipulating na cells na living organisms a kawo cututtuka, wanda sun fara kirkiro su ne, sun samu idea na yinsu ne tun lokacin annobar cutar “Bubonic Plague”, sannan sun fara kirkiro shi ne lokacin da akayi yakin duniya na farko (First World War), wanda Kasar Jamani ita ta fara, ta samar da ciwon “Anthrax”, sannan kuma ta kara modifying na Organisms na bacteria mai kawo cutar “Cholera”
Sannan ta kara kirkiran wani cutar “Fungi” wanda ke kashe alkama, wannan alkama da muka sani, don haka suka turashi idan kunyi noma sai a tura wannan kwayar cuta na “Fungi” duka sai ya lalata amfanin gonar, ku wayi gari cikin yunwa, Biological Weapons din ba sai akan ‘dan-adam ba, har abinda kuke noma, da koramu da tekunan ruwa, idan kuna da kifaye duka ana iya saka muku Biological Weapons a kashe su
Kasar Iland a da sunfi kowa noman dankalin turawa (Irish potato) a duniya, sai aka tura musu da wani kwayar cutar “Fungi” yaje ya lalata musu dankalin gabaki daya, daga baya sai da sukayi wata irin mutuwa aka dinga mutuwa saboda tsananin yunwa, saboda sun dogara ga noman dankalin, suna nomawa su sayar su sayo abinci suci, miliyoyin mutane suka mutu, miliyon mutane suka bar gidajensu, har gobe idan kaje Kasar wannan tarihin bai bace musu ba, kuma idan ka laluba directly ko indirectly Amurka na da hannu cikin abinda aka musu
Don haka wannan shine aikin yahudu da nasara, babban maganinsu garemu Musulmi shine muyi hakuri mu koma ga Allah, sannan duk abinda zamuyi to muyishi tsakanin mu da Allah, Malamai suji tsoron Allah su karantar damu gaskiya, sa’annan su koyar damu abinda zamu aikata idan musiba tazo, da addu’ah da zamu dingayi saboda wannan masifar, domin bala’i ne wanda ba karami ba.
Ciwo ne wanda matsalarshi shine saurin yaduwa, sa’annan yana wahalar da ‘dan-adam, yana kisan ‘dan-adam, sa’anann yana kawo ma ‘dan-adam matsaloli da dama, akwai wanda zai warke, bayan ya warke amma kwakwalwarshi ba zata koma dari bisa dari yadda take ba, saboda abin ya shafi numfashi, bai iya kai iska zuwa ga kwakwalwa, wasu cells daga cikin kwakwalwa zasu mutu, idan sun mutu kuma ba za’a taba canza su ba, don haka mutum zai rasa wani abu cikin kwakwalwarshi
Nan gaba za’a samu mutane miliyoyi suna rayuwa amma basa iya ajiye karatu cikin kwakwalwarsu, saboda wannan cutar, don haka wannan ciwon na Coronavirus ko an gamashi za’ayi shekaru aru-aru ana fama da matsalar, abinda ka sani ya bace maka, kwakwalwarka bata iya daukan karatu, zata kasance bata da zarafi na yin abinda ta saba yi kafin kamuwa da wannan cutar, wannan kunga ba karamin bala’i bane, don haka ire-iren wadannan abubuwan duka sai mun gansu ga hannun yahudu
Wani zaice to ai ga Amurka can ana mutuwa, to mai wannan tunanin don Allah yaje ya karanta abinda ake kira da “World Totalitarian Government” ko kuma “New World Order” “Nazmul aalam al-jadidi”, duk mai shakku yaje ya karanta wannan zai bawa kanshi amsa, idan mutum Milyan dari sun mutu a Amurka hankalinsu bai tashi, Amurka ba itace burinsu ba, burinsu dabam, idan an kashe ba’amurke guda kaga hankalinsu ya tashi sun dauki yaki, idan ka karanta tsarinsu na New World Order zaka fahimci makircin
Yaa Allah Ka tsare mana Malam Bashir Ahmad Sokoto daga sharri da makircin yahudawa da munafukai, Allah Ka kare al’ummar Musulmi gabaki daya Amin
Ga lin nan domin saukar da wannan darasin tafsir ku saurara da kunnuwan basira.
Kuma ku tura zuwa ga yan uwa musulmi domin amfana
Recommended:  Abubakar Sani - Asharalle

Download MP3 Now

Prev Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *